Kungiyar Yan Jaridu a jihar Jigawa ta nemi ana sanya yan kungiyar cikin tsarin rabon tallafin rage radadi

0 145

Kungiyar Yan Jaridu ta kasa reshen jihar Jigawa ta koka akan rashin sanya yan kungiyar cikin tsarin rabon tallafin kayayyakin rage radadin cire tallafin man fetir a matakin jiha da kananan hukumomi.

Shugaban kungiyar, Comrade Garba Muhammad Bulangu ya bayyana hakan a lokacin rangadin duba wasu cibiyioyin rabon tallafin a jihar nan.

Comrade Garba Bulangu ya ce shigo da yan Jaridu cikin tsarin rabon tallafin zai kara tabbatar da yin gaskiya da adalci da kuma wayar da kan alumma muhimmancin yiwa gwamnati godiya kan bada tallafin. Bayan ya yabawa kokarin gwamna Umar Namadi na samar da kayayyakin masarufi da kuma tallafin kudade ga alumma domin rage musu radadin cire tallafin man fetir, kungiyar ta jaddada kudirinta na mara baya ga kyawawan manufofin gwamnatin jiha na ciyar da alummar jihar nan gaba

Leave a Reply

%d bloggers like this: