Gwamnatin jihar Jigawa tace zata fifita muradun alumma wajen tsara kasafin kudin 2024

0 238

Kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki Alhaji Babangida Umar Gantsa ya sanar da hakan a lokacin taron tattaunawa kan tsara kasafin kudin badi da masu ruwa da tsaki.

Yace an shirya taron ne na hadin gwiwa domin tattara bayanai da bukatun alumma wajen tsara kasafin kudin shekara mai zuwa.

Alhaji Babangida Umar Gantsa ya bayyana cewar gwamnatin tana amfani da bukatun alumma wajen tsara duk wani kasafin kudi.

A nasa jawabin Daraktan gudanarwa na shirin tabbatar da jagoranci, Comrade Isah Mustapha ya bukaci alumma dasu bada bayanai mai ma’ana domin sanyawa a cikin daftarin kasafin kudi da nufin baiwa gwamnati damar yin aiyukan da alumma ke bukata. Ya kuma yabawa ma’aikatar kasafin kudi bisa shirya taron tattaunawar domin alumma su bada tasu gudunmawa wajen tsara kasafin kudi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: