Hukumar kula da filayen Noma ta kasa ta kaddamar da biyan kudade ga manoma jihar Jigawa

0 349

Hukumar kula da filayen Noma ta kasa a jihar Jigawa ta kaddamar da biyan kudade ga manoman da suka shiga shirin noman alkama a fadin jihar.

Kantoman Hukumar a jihar Jigawa, Mallam Bello Umar Kazaure ya sanar da hakan, inda yace hukumar ta noma hecta 200 ta alkama, yayinda manoman alkama 300 suka shiga cikin shirin noman alkama a 2022.

Yace an gudanar da noman alkamar ne a wuraren noman Rani dake yankunan kananan hakumomin Roni, Ringim, Miga da kuma Hadejia.

Mallam Bello Umar ya kuma yabawa kokarin manoman na alkama a madadin sakataren zartarwa na hukumar ta kasa.

Ya kuma bada tabbacin hukumar na cigaba da bunkasa aikin noma a fadin jiha.

Leave a Reply

%d bloggers like this: