‘Yan bindiga sunyi garkuwa da dalibai mata a jami’ar gwamnatin tarayya dake Dutsin-Ma

0 249

Akalla dalibai mata biyar a jami’ar gwamnatin tarayya dake Dutsin-Ma ta jihar katsina ‘Yan bindiga sukayi garkuwa da su.

Rundunar yan sandan jihar ta kama mutum 1 da ake zargin yana da hannu a satar yaran.

An sace daliban ne a gidajen su dake kusa da makarantar Ajiri Memorial International School akan hanyar Tsakiya.

Mai magana da yawun yan sandan  jihar SP Abubakar Sadiq ne ya tabbatar wa manema labarai faruwan lamarin.

Ya bayyana cewa sun kama wani da ake zargi yana da hannu a faruwar lamarin. Ya kara da cewa har yanzu ana gudanar da bincike domin  ceto yan matan daga hannun yan bindigar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: