Gwamnatin Najeriya zata sanya yara kimanin Milyan 10 a makaranta

0 184

Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin ta na sanya yara kimanin Milyan 10 da basa zuwa makaranta a shiyyoyi 6 dake kasar nan, nan da makonni kalilan.

Karamin Ministan Ilimi Yusuf Sununu shine ya bayyana haka a Abuja, a lokacin da ya karbi bakuncin tsoffin yan Majalisa na jam’iyyar APC mai mulki.

Toshon mataimakin kakakin majalisar wakilai Babangida Nguroje, wanda ya jagoranci tawagar ya ja hankalin karamin Ministan Ilimin dangane da bukatar baiwa fannin ilimi fifiko musamman ga marasa karfi.

Kazalika ya bukaci karamin Ministan da ya kawo cigaba yadda ya kamata domin shigar da kananan yara a makarantu. Yace babu kasar da zata ciga face sai ta baiwa fannin ilimi fifiko.

Leave a Reply

%d bloggers like this: