Sojojin kasar Indiya 23 ne suka bata sanadiyyar ambaliyar ruwa

0 242

Akalla sojojin kasar Indiya 23 ne suka bata biyo bayan ambaliyar ruwa data afkawa jihar Sikkim dake arewa maso gabashin kasar.

Sojojin kasar sun ce ambaliyar ruwa ta faru ne biyo bayan sakin ruwa na Dam din Chungtahng wanda yayi cika sosai.

Ambaliyar ruwa ba bakuwa bace a irin wanna lokaci a kasar Indiya, musamman daga watan Yuli zuwa Oktoba, lamarin dake yin kamari sosai a kasar.

Masana sunce sauyin yanayi na kara ta’azzara al’amura a kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: