Gwamnatin Jigawa zata hada kai da rundunar sojojin kasar nan domin samar da tsaro a jiha

0 265

Gwamnatin jihar Jigawa tayi alkawarin hada kai da rundunar sojojin kasar nan domin samar da tsaro da zaman lafiya a jihar nan.

Gwamna Malam Umar Namadi ya fadi haka ne yayinda ya karbi bakuncin babban kwamandan sojoji na Jihar Kaduna, Manjo Janar B Okoro jiya a Dutse.

Malam Umar Namadi ya bayyana lamarin tsaro a matsayin abu mai mahimmanci,inda yayi alkawarin baiwa hukumomin tsaro goyan baya domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Tunda farko Okoro, ya taya Gwamnan murnar zabar sa a matsayin gwamnan jihar Jigawa. Ya kuma yiwa jihar Jigawa alkawarin samar da tsaro yadda ya kamata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: