Sanata Ahmad Lawan ya ce babu bukatar mutane su tayar da jijiyar wuya game da karbar tubabbun ’yan Boko Haram

0 262

Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Ahmad Lawan ya ce babu bukatar mutane su tayar da jijiyar wuya game da karbar tubabbun ’yan Boko Haram.

Ya ce ajiye makamai da Boko Haram ke yi wata nasara ce da ya kamata a karbe ta hannu bibbiyu, domin hakan na nuni da cewa ta’addanci ya kusa zuwa karshe.

Ya kara da cewa Tuban yan kungiyar Boko Haram wata nasara ce ga Gwamnatin Tarayya da kuma Gwamnatin Jihar Borno na kawo karshen zubar da jinin da aka dade ana yi.

Sanata Ahmad Lawan ya bayyana haka ne a Maiduguri, yayin ziyarar da ya kai Fadar Shehun Borno, Abubakar El-Kanemi, jiya Litinin kamar yadda hadiminsa kan kafafen watsa labarai ya sanarn.

Shugaban Majalisar ya kai ziyarar ne don yin jaje da ta’aziyya ga Shehun kan rasuwar dan uwansa Ambasada Babagana Kingibe.

A cewarsa, daga cikin tubabbun ’yan Boko Haram din da aka gano ba su da matsala, za’a mayar da su cikin al’umma don ci gaba da rayuwa, wadanda kuma aka gano suna da matsala za’a bi hanyar da shari’a ta gindaya a kan irinsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: