Sanata Shehu Sani ya gargadi Bola Tinubu kan maimaita irin kuskuren Buhari ya tafka a baya

0 138

Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya gargadi shugaban kasa Bola Tinubu kan maimaita irin kuskuren da tsohon shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tafka a fannin nade-nade. Shehu Sani yace, ba kamar Buhari ba, nade-naden da Tinubu zai yi yamata su zama bisa cancanta. Da yake jawabi a gidan talabijin na kasa, tsohon dan majalisar ya kalubalanci Buhari da nuna wariya yayin da ke rike da mukamin shugaban kasa. Shehu Sani jaddada cewa wariya da nuna banbancin ya kai makura, yana mai mamakin dalilin da ya sa wani ministocin suka kwashe shekaru 8 suna aiki karkashin mulkin Buhari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: