Sarkin Musulmai ya umurci a fara duban jinjirin watan Al-Muharram

0 330

Mai alfarma Sarkin Musulmai Sa’ad Abubakar III, a jiya ya umurci al’ummar Musulmi da su fara duban jinjirin watan Al-Muharram daga yau Litinin.

Sarkin Musulmi, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta kasa , ya ba da umarnin a cikin wata sanarwa da kwamitin ba da shawara kan harkokin addinin musulunci dake Sokoto ya fitar a jiya.

Sarkin Musulmin ya yi addu’ar Allah ya taimaki dukkan musulmi wajen gudanar da ayyukansu na addini.

Idan zamu iya tunawa dai watan Muharram shi ne watan farko na kalandar Musulunci, kuma guda ne cikin watanni musulunci masu albarka da alfarma a kowacce shekara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: