Manoma sun gudanar da addu’o’i saboda rashin samun ruwan sama

0 308

Kamfanin Dillancin Labarai Kasa NAN ya bayar da rahoton cewa, manoman da galibinsu suke zaune a yankunan arewaci da tsakiyar jihar Borno, sune wadanda karancin ruwan yafi shafa a halin yanzu.

A yau ake tsammanin zasu fita domin yin addu’o’in neman taimakon Allah wajen rokon ruwan sama.

Manoman da dama da suka fito daga kananan hukumomin Maiduguri, Jere, Konduga, Kaga da Mafa sun ce karancin ruwan ya tayar musu da hankali  saboda babu wata hanyar da suka Dogara ta ita face noma.

Wannan na zuwa ne adaidai lokacin Majalisar Masarautar Borno ta fara jan hankalin jama’a domin gudanar da addu’o’in samun ruwan sama. Sanarwa daga Shehun Borno, Alhaji Abubakar Umar Garbai El-Kanemi ya bayar, ta bukaci al’ummar Musulmi da su hallara a dandalin Ramat Maiduguri a yau domin yin addu’ar samun ruwan saman.

Leave a Reply

%d bloggers like this: