An kama wasu mutane biyu da ake zargi da mallakar jabun dalar Amurka

0 281

Jami’an tsaron farin kaya ta kasa Civil Defence reshen jihar Jigawa sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da mallakar jabun dalar Amurka dubu 30 da dari 9

Kakakin hukumar CSC Adamu Shehu ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da wadanda ake zargin jiya, a hedikwatar rundunar da ke Dutse babban birnin jihar.

Wadanda ake zargin sun hada da, Danladi Umar mai shekaru 25 dan Tashar Musawa, karamar hukumar Zaria jihar Kaduna da Abdurrahman Khalid  mai shekara 35.

A cewarsa, an kama wadanda ake zargin ne a lokacin da wani Danladi Umar ya shigar da karar cewa wani Abdurrahman Khalid ya yaudare shi tare da damfarar sa ta hanyar alakanta shi da wani Malami da ya karbo kudi Naira dubu 147 da dari 5 don bashi asiri. Kawo yanzu dai dukkanin su sun amince da aikata laifukan da ake zarginsu tare da bawa Jamian tsaro hadin kai wajen gudanar da binciken su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: