Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bayyana damuwarsa kan yadda sha’anin rigakafi ke samun tangarda ga yaran Arewa sakamakon rashin tsaro da wasu dalilai.
Sarkin Musulmi a jiya a Kaduna ya jagoranci wani muhimmin taro tare da sarakuna da shugabannin gargajiya da kuma abokan ci gaba domin tsara hanyoyin da za a bi.
Taron wanda hukumar kula da lafiya matakin farko ta kasa ta shirya tare da hadin guiwar gidauniyar zaman lafiya da ci gaba ta Sultan Foundation ya tattauna kalubalen da ke hana yaran arewa samun rigakafi.
Wakilan Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna Hadiza Sabuwa Balarabe da sauran masu ruwa da tsaki sun halarci taron.
Sarkin ya nanata kudurin sarakuna na tabbatar da cewa al’umma sun ci gajiyar shirin riga-kafi na yau da kullum. Sarkin Argungu, Alhaji Sama’ila Muhammad Mere, wanda shi ne shugaban kwamitin sarakunan gargajiya na Arewa kan harkokin kiwon lafiya a matakin farko, ya ce bukatar kiran wannan taro ta samo asali ne daga rahoton halin da ake ciki da aka samu a taron bita na farko na NTLC daga Zamfara.