Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin sanya sabbin takunkumi  kan gwamnatin mulkin soji a jamhuriyar Nijar

0 175

Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin sanya sabbin takunkumi ta hannun babban bankin Najeriya kan hukumomi, da daidaikun mutane da ke da alaka da gwamnatin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a Ajuri Ngelale wanda ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a jiya, ya ce wadannan takunkuman sun ta’allaka ne kan matakin takunkumin kudi da kungiyar ECOWAS ta yi wa gwamnatin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar.

A cewarsa, duk da cewa babu wani zabi da aka cire daga teburin tattaunawar, ana sa ran kungiyar za ta yanke hukunci mai tsauri a wani taro na musamman da za a yi gobe Alhamis a Abuja.

Ya kara da cewa babu wani zabi da aka cire daga teburin, amma Tinubu da sauran shugabannin Afirka ta Yamma suna goyon bayan diflomasiyya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: