Gwamnatocin sojojin Mali da na Burkina Faso sun tabbatarwa da jagororin juyin mulkin sojan Nijar cikakken goyon bayansu

0 264

Tawagar gwamnatocin sojojin Mali da na Burkina Faso sun tabbatarwa da jagororin juyin mulkin sojan Nijar cikakken goyon bayansu a ziyarar hadin kai da suka kai wa Janar Abdourahamane Tchiani a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar ta Ecowas ke shirin gudanar da wani taro a yau Alhamis domin tattaunawa kan matakin da za a dauka na yaki da gwamnatin Nijar.

Wa’adin da kungiyar Ecowas ta bayar na mayar da shugaban kasar Mohamed Bazoum a ranar Lahadin da ta gabata, shugabannin sojojin Nijar sun yi biris da shi, har yanzu ana tsare da shi.

Kakakin gwamnatin mulkin sojan Mali Abdoulaye Maiga a ranar Litinin ya bayyana takunkumin da kungiyar Ecowas ta kakabawa Nijar a matsayin wanda ya sabawa doka, haramun ne kuma rashin mutuntaka.

Ya ce Burkina Faso, Mali da Nijar sun shafe shekaru goma suna fama da munanan sakamako na zamantakewa da tattalin arziki, tsaro, siyasa da kuma jin kai.

Wakilin na Mali ya kuma karfafa gwiwar ‘yan Nijar da su kasance masu juriya da hakuri a cikin wadannan lokuta masu wahala tare da ba su tabbacin samun nasara da goyon bayansu.

Shugabannin sojojin Mali da Burkina Faso a makon da ya gabata sun yi gargadi game da tsoma bakin sojojin Ecowas a Nijar, suna masu cewa hakan na nufin shelanta yaki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: