Jami’ar Diflomasiyyar Amurka ta kai ziyara jamhuriyar Nijar sun yi ganawa mai tsauri da jagororin juyin mulki

0 197

Babbar jami’ar Diflomasiyyar Amurka Victoria Nuland da ta kai ziyara jamhuriyar Nijar, ta ce sun yi ganawa mai tsauri da jagororin juyin mulki.

Ta ce sun ki amincewa ta gana da shugaba Muhammad Bazoum.

Shi kuwa Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce Amurkan na goyon bayan matakin da ECOWAS ke ɗauka domin mayar da mulkin dimokraɗiyya Nijar, da bukatar sakin Bazoum da mukarraban gwamnatinsa da ake tsare da su.

Mis Nuland ta kara da cewa duk da ba su amince da miƙa mulkin ga farar hula ba, amma sun amince kan hatsarin da ke cikin shigowar sojin haya na Wagner da ke ayyuka a ƙasashe makwaɓtanta wato Mali da Burkina Faso.

Leave a Reply

%d bloggers like this: