Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci jakadun kasarnan da aka nada da su cigaba da yada bangarorin da Najeriya take da karfi tare da nuna inda gwamnati tafi mayar da hankali da kuma tsayawa akan manufofi masu kyau wadanda zasu karawa kasarnan kima.

Shugaba Buhari ya bayar da umarnin ne ta bidiyo a wajen taron kaddamarwa da wayar da kai, da aka shirya musu a dakin taro na hukumar leken asiri ta kasa.

Ya kuma hore su da su dage wajen inganta kasuwanci da gina rayuwar dan adam, da kawo masu zuba jari daga kasashen waje da wasu bangarorin hadin kai da kasashe a matakan kasa da wajen taruka na duniya, domin taimakawa cigaban kasa. Shugaban kasa ya kuma bayyana bangarorin da aka mafi mayar da hankali da suka hada da gina tsarin da zai yaki rashawa da inganta aikin gwamnati da kuma inganta tsaro domin kowa da kowa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: