Shugaba Buhari ya fara kaddamar da shirin bayar da tallafin noman rani na dala miliyan 73

0 147

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya fara kaddamar da shirin bayar da tallafin noman rani na dala miliyan 73, domin habaka shirin samar da sukari da nufin mayar da Najeriya a matsayin kasa mafi samar da sukari a nahiyar Afrika.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN, ya bayar da rahoton cewa, domin tabbatar da wannan mafarkin, an kuma rattaba hannu kan wata yarjejeniya tsakanin gwamnatin tarayya da masu gudanar da shirin hadin gwiwa na baya-bayan nan na samar da sukari a ranar 21 ga watan Disamba a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Da yake jawabi a wajen taron, Ministan Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, Mista Niyi Adebayo, wanda ya wakilci Shugaba Buhari, ya ce babban bankin kasa (CBN) na daga cikin wadanda zasu samar da kudaden da ake bukata domin gudanar da shirin.

A cewar Adebayo, manufar shirin ita ce a kara yawan sukarin da Najeriya ke samarwa, a daidai lokacin da take kokarin dogaro da kanta wajen samar da Sukari.

Shima da yake jawabi a wajen taron, Sakataren Zartaswa na Majalisar samar da Sukari ta kasa, Mista Zacch Adedeji, ya ce tallafin wani bangare ne na kudirin gwamnati na samar da yanayi mai kyau ga masu zuba Jari su samu cigaba da bunkasa a kasarnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: