Shugaba Buhari ya kaddamar da dalar shinkafa mafi girma a nahiyar Afirka

0 183

Hakan ya samu ne sanadiyyar gagarumar nasarar da aka samu a shirin bayar da lamuni na babban bankin kasa (CBN) tare da hadin gwiwar manoman shinkafa da masu sarrafata da gwamnatocin jihoshi tare da sauran masu ruwa da tsaki.

Manyan bakin da ake sa ran zasu halarci bikin sun hada da shugabannin kasashen jamhuriyar Beni da Nijar da Chadi, tare da gwamnonin jihoshin Jigawa, Kebbi, Sokoto, Ekiti, Cross River da Ebonyi.

Kungiyar manoman shinkafa ta kasa (RIFAN) cikin wata sanarwa tace za tayi amfani da bikin wajen kaddamar da shirinta na noman shinkafa ‘yar rani na shekarar 2021 zuwa 2022, tare da gudanar da bikin shinkafa na shekara-shekara.

An kaddamar da shirin bayar da lamuni na CBN a shekarar 2015 a jihar Kebbi a matsayin wani shiri na musamman da nufin bunkasa noman shinkafa a cikin kasa tare da nufin rage yawan kudaden da ake kashewa wajen shigo da ita daga kasashen waje.

Leave a Reply

%d bloggers like this: