Shugaba Buhari Ya Sanya Sabuwar Doka Ga Yan Siyasa A Filayen Jirgi

0 69

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayar da dama ga ma’aikatar sufurin jiragen sama ta tarayya da ta hana dukkan hadiman masu rike da mukaman siyasa da sauran manyan mutane daga shiga wajen zaman jira a filayen jiragen sama.

A cewar ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, an haramtawa dukkan hadiman manyan mutane zuwa filayen jiragen sama, matukar ba iyayen gidansu ne za suyi tafiya ba.

Hadi Sirika ya kuma bayyana cewa dukkan fasinjan da yaki sanya abin rufe baki da hanci, baza a kyale shi ya hau jirgin sama ba, bayan an dawo da jigilar jiragen saman a gobe, farawa da filayen jiragen saman Abuja da Lagos.

Ministan ya sanar da haka a taron manema labarai na kwamitin karta kwana na shugaban kasa akan cutar corona a Abuja. A cewarsa, ba a amince da zuwa da makamai filayen jiragen sama ba.

Akan ko za ake bayar da tazara a cikin jiragen sama, Hadi Sirika yayi bayanin cewa babu wata barazana a dakunan jiragen sama, inda ya bayyana iskar cikin jiragen sama a matsayin tsaftatacciya wacce aka tace.

Leave a Reply

%d bloggers like this: