Shugaba Tinubu ne kadai zai iya zabar abokin takararsa a 2027 — APC reshen Arewa maso Gabas

0 151

Jam’iyyar APC reshen Arewa maso Gabas ta bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne kadai ke da ikon zabar abokin takararsa a zaben 2027.

Wannan na zuwa ne bayan taron da jam’iyyar ta gudanar a ranar Lahadi a Gombe, inda aka nuna goyon baya ga Tinubu, ba tare da ambaton mataimakinsa, Kashim Shettima ba.

Taron ya haifar da cece-kuce, inda wasu suka zargi cewa ana kokarin maye gurbin Shettima, musamman ganin yadda shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje, da wasu shugabanni suka gaza ambaton sunansa a jawabansu.

Sai dai APC ta bayyana cewa goyon bayan da aka bai wa Tinubu ba ya da sharadi, kuma zaben Shettima a matsayin abokin takara ya rage ga Tinubu, kamar yadda jaridar Premium Times ta ayyana.

Leave a Reply