Shugaban INEC ya bayyana cewa zabukan da ke tafe na fuskantar barazanar sokewa ko dagewa idan har ba a samu sauki a kalubalen tsaro ba

0 117

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, a jiya ya bayyana cewa zabukan da ke tafe na fuskantar barazanar sokewa ko dagewa idan har ba a samu sauki a kalubalen tsaro da ake fuskanta a fadin kasar nan ba.

Mahmood Yakubu wanda shugaban cibiyar zabe Abdullahi Zuru ya wakilta ya yi jawabi a wajen tabbatar da horo kan harkokin tsaro yayin zaben da aka gudanar a Abuja.

Ya yi nuni da cewa, zabukan dake tafe na fuskantar babbar barazana ta sokewa idan har al’amuran tsaro suka kasa inganta a fadin kasar nan.

Sai dai shugaban na INEC ya tabbatar wa duk masu ruwa da tsaki cewa hukumar za ta yi duk iyawarta wajen ganin an samar da tsaro ga jami’an zabe da kayan aiki.

Ya ce hukumar ta INEC ta yaba da yadda tsaro ke da matukar muhimmanci lokacin zabe wajen tabbatar da dimokuradiyya ta hanyar samar da yanayi na gudanar da zabe mai inganci, na gaskiya, kuma sahihi wanda hakan zai karfafa tsarin zabe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: