Shugabancin kungiyoyin NLC da TUC da kungiyar ‘Yan Fansho sun yabawa gwamna Uba Sani

0 156

Shugabancin kungiyoyin kwadago na NLC da TUC da kungiyar ‘Yan Fansho a Jihar Kaduna, sun yabawa gwamnan jihar Uba Sani sakamakon sakin kudi kimanin Naira Bilyan 3.1 domin biyan ‘Yan Fansho da Iyalan wadanda suka mutu hakkokin su.

Kungiyoyin kwadagon sun godewa gwamna Uba Sani bisa sakin kudin akan lokaci, musamman la’akari da halin matsin tattalin arziki da ake ciki.

A cewar kungiyoyin uku,biyan ‘Yan fansho da Iyalan wadanda suka mutu hakkokin su, hakan zai rage radadin tsadar rayuwa da ake ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: