Shugaba Tinubu na kokarin inganta rayuwar ‘Yan Najeriya marasa galihu – Shettima

0 225

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, yace shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na kokarin inganta rayuwar ‘Yan Najeriya marasa galihu.

Kashim Shettima ya fadi haka a fadar shugaban kasa dake Abuja yayin da yake karbatar rahotan kwamitin magance ambaliyar ruwa.

Shettima ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya maida hankali domin inganta zaman takewar mutane masu karamin karfi a Najeriya. Mataimakin shugaban kasa da yake karbar rahotan kwamitin,yace kwamitin ya samu bayanai daga hukumar hasashen yanayi ta kasa da sauran hukumomin da lamarin ya shafa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: