Shugabannin jihar Borno sun amince da dawowar tubabbun mayakan Boko Haram zuwa cikinsu

0 106

Shugabannin al’umma a jihar Borno a jiya sun amince da dawowar tubabbun mayakan Boko Haram zuwa cikinsu.

An dauki matakin a wajen taron masu ruwa da tsaki domin tattaunawa dangane da yawaitar kalubalen tsaro a jihar. Gwamnatin jihar Borno ce ta shirya zaman ganawar.

Gwamnatin jihar Borno ta tabbatar da cewa akalla mutane dubu 3 ne wadanda a baya suke ‘yan kungiyar ta Boko Haram suka ajiye makamansu, inda suka mika wuya ga sojojin Najeriya.

Gwamna Babagana Zulum, wanda ya jagoranci zaman ganawar, ya sanar da cewa baya ga tubabbun mayaka dubu 3 da a yanzu suke hannun gwamnati, karin wasu ‘yan Boko Haram 900 sun mika wuya ga dakarun kasar Kamaru.

Gwamna Zulum yace zaman ganawar masu ruwa da tsakin ya zama tilas biyo bayan cece-kucen da ake yi a ‘yan kwanakinnan sanadiyyar mika wuyan da dumbin mayakan Boko Haram suke yi.

Zulum yace akwai bukatar gwamnati da shigo da dukkan masu ruwa da tsaki a jihar Borno, a tsare-tsaren daukar mataki dangane da yadda za ayi da tubabbun mayaka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: