Sojin Najeriya sun halaka ‘Yan bindiga 3 da kwace bindiga kirar AK47 da alburusai a jihar Kaduna

0 170

An kashe ‘Yan bindigar ne a yankin Maidaro, Ngade, Ahla da Rikau dake karamar hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna.

Mai magana da yawun rundunar dakarun sojin Najeriya a jihar Kaduna Musa Yahaya, yace wasu ‘Yan bindiga sun tsere yayin artabu wasu kuma sun gudu da harbin bindiga a jikin su.

Musa Yahaya yace sun samu nasarar kwato wasu kayan sata da motoci a hannun ‘yan bindigar.

Ya kuma kara da cewa dakarun sojin kasar nan sun gudanar da ayyukan kakkabe yan ta’adda a karamar hukumar Chikun da kewaye.

Kazalika, yace babban kwamandan rundunar dakarun a Jihar Kaduna Valentine Okoro, ya yabawa sojojin bisa wannan babban aikin da suka yi. Valentine Okoro, ya bukaci al’ummar Jihar Kaduna da suci gaba da baiwa sojoji da hukumomin tsaro bayanai domin yaki da ‘Yan ta’adda.

Leave a Reply

%d bloggers like this: