Sojoji sun kashe wasu ‘yan bindiga uku a wani samame da suka kai maboyar su

0 292

Dakarun rundunar ‘Operation Whirl Punch’ na sojojin Najeriya sun kashe wasu ‘yan bindiga uku a wani samame da suka kai maboyar su da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna.

Wata sanarwa da mukaddashin darakta mai kula da hulda da jama’a na rundunar soji ta daya reshen rundunar sojan Najeriya Musa Yahaya ya fitar, ta ce sojojin sun kwato bindigogi kirar AK-47, dana gida guda biyu, da wasu bindigogi guda bakwai, da kuma babura guda takwai a lokacin aikin.

Ya kara da cewa sauran kayayyakin da aka kwato sun hada da bindigogi guda uku da aka yi a gida, da wayoyin hannu guda shida, magunguna, da kuma laya.

A halin da ake ciki, Babban Jami’in Gudanarwa na rundunar Major General BA. Alabi, ya yabawa dakarun da suke yi, ya kuma bukace su da su ci gaba da kai farmaki har sai an kawar da duk masu aikata laifuka gaba daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: