Sojoji sun kuɓutar da mutane 16 da ƴan bindiga suka sace a yankin Kajuru da ke jihar Kaduna

0 134

Rundunar sojoji ƙarƙashin runduna ta ɗaya sun kuɓutar da mutane 16 da ƴan bindiga suka sace a yankin Kajuru da ke jihar Kaduna.

Sun kuma daƙile yunƙurin wata ƙungiyar miyagu na yin garkuwa da mutane.

Cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na rundunar sojin, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, rundunar ta ce sojojin da aka tura ƙarƙashin runduna ta ɗaya sun daƙile yunƙurin sace mutane tare da ceto mutanen da aka sace a yankin Tantatu da ke ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.

A cewar sanarwar, sojojin sun kai samamen ne bayan bayanan sirrin da suka samu a ranar Lahadi da daddare lokacin da suka bi sawun ƴanbindigar da suka sace wasu mutane a ƙauyen. Shugaban hafsan sojojin ƙasa Taoreed Lagbaja ya yabawa sojojin kan ƙoƙarin nasu tare da neman su ƙara ƙaimi wajen fatattakar masu aikata ta’addanci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: