Sojojin hayar Rasha za su ci gaba da ayyukansu a ƙasashen Afirka

0 339

Shugaban Kamfanin sojojin hayar Rasha na Wagner Yevgeny Prigozhin ya shaida wa gidan talbijin na ‘Afrique Media TV’ cewa sojojinsa za su ci gaba da ayyukansu a inda suke a yanzu a ƙasashen Afirka

Mista Prigozhin ya ce ƙungiyar ba ta da niyyar rage ayyukanta a Afirka.

Kalaman nasa na zuwa ne bayan samun raɗe-raɗin janye dakarun ƙungiyar daga ƙasashen Mali da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, bayan taƙaitaccen boren da ƙungiyar ta yi a Rasha ranar 24 ga watan Yuni. Kungiyoyin kare hakkin bil-adama na zargin dakarun Wagner da keta hoƙƙokin bil-adama a Mali da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka

Leave a Reply

%d bloggers like this: