Sojojin Najeriya zasu iya yin kuskure – Janar Christopher Musa

0 242

Babban Hafsan tsaro na kasa Janar Christopher Musa yayi kira ga ‘Yan Najeriya su baiwa dakarun sojojin kasar hadin gwiwa, yana mai cewa gwiwar su baza tayi sanyi ba sakamakon harin da kai Jihar Kaduna.

Kimanin mutane 85 harin jirgin saman maras matuki na sojin kasar nan ya halaka tare da jikkata mutane da maa a karamar hukumar Igabi dake jihar.

Ammma babban Hafsan tsaron na kasa ya bayyana cewa sojojin kasar nan zasu iya yin kusure, yana mai kira ga ‘Yan kasar nan su baiwa sojojin hadin kai domin yaki da matsalar tsaro a fadin kasar nan.

Tunda farko dai rundunar sojojin kasar nan ta nemi afuwa kan wannnan lamari, inda ta bayyana shi a matsayin abun takaici. Manyan mutane mabambanta, da kuma jami’an gwamnati ciki hadda mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima sun kai ziyara garin da aka kai wannan hari tare da  basu tallafi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: