Ana kokarin dakatar da ficewar babban shagon siye-siye na Shoprite daga Kano

0 223

Mataimakin shugaban majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin yace yana kokarin dakatar ficewar babban shagon siye-siye na garin Kano Shoprite, wanda shine reshen su daya tilo a Jihar.

Wannan na zuwa ne bayanda shagon na Shoprite ya sanar da ficewar daga Jihar Kano a watan Janeru shekara mai zuwa biyo bayan kalubalan tattalin arziki da ake fama da shi.

Hadimin Sanata Barau Jibrin a kafafan yada labarai Ismail Mudashir, yace mataimakain shugaban majalisar Dattawan ya shirya ganawa da shugabancin Kamfanin cikin wannan mako a Abuja.

Idan dai za’a iya tunawa a makon da ya gabata ne babban Kamfanin Procter & Gamble, ya sanar da cewa yana shirye-shiryen ficewa daga Najeriya.

Tunda farko, Kamfanin GlaxoSmithKline Consumer Nigeria plc shima ya sanar da janyewar sa daga kasar nan. Kungiyar masu Kamfanoni ta kasa ta nuna damuwar cewa akwai karin wasu shagunan saida kayayyaki da zasu fice daga kasar nan sakamakon matsin tattalin arziki da ake fama da shi a kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: