An samu rahotannin hatsari kimanin 231, yayin da mutane 205 suka mutu a jihar Kano

0 196

Hukumar kiyayye haddura ta kasa, tace ta samu rahotannin hatsari kimanin 231, yayin da mutane 205 suka mutu a jihar Kano kadai, daga watan Janeru zuwa Nuwambar wannan shekarar.

Shugaban hukumar na Jihar Ibrahim Abdullahi,shine ya sanar da haka ga kamfanin dillancin labarai na kasa a Kano.

Ibrahim Abdullahi,yace kimanin mutane 1,451 ne haddura ya rutsa da su, yayin da mutane sama 759 suka samu muna-nan raunuka, inda hukumar ta samu nasarar ceto mutane 692 da sukayi hatsari.

Ya kara da cewa kimanin ababan hawa 33,324 suka kwace sakamakon keta dokokin amfani da hanya.

Ya bayyana wasu daga cikin laifukan da suka aikata kamar,rashin mallakar lasisin tuki, lodin da wuce kima da kuma gudun wuce gona da iri. Shugaban hukumar a Jihar Kano,ya bukaci masu amfani da motoci suna kiyaye dokokin hanya tare da yin amfani da Danjar da ke tsayar da ababan hawa domin tabbatar da lafiyar mutane akan hanya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: