Gwamnatin Jihar Gombe ta sha alwashin hukunta duk wanda aka samu da laifin cin zarafin kananan yara

0 203

Gwamnatin Jihar Gombe ta sha alwashin hukunta duk wanda aka samu da laifin cin zarafin kananan yara a jihar.

Kwamishiniyar kula da harkokin mata ta Jihar Asma’u Muhammad Iganus, ita ce ta bayyana haka bayanda gwamnan Jihar Muhammad Inuwa Yahaya ya sanya hannu kan dokar hukunta masu cin zarafin kananan yara.

Asma’u Iganus tace baza tayi kasa a gwiwa wajen neman goyan bayan masu ruwa da tsaki a kokarin da take na yaki da cin zarafin kananan yara.

Da take zantawa da manema labarai yayin kaddamar da kwamitin kare hakkin kananan yara mai Mambobi 38 a Gombe,kwamishiniyar tace duk wani mai aikata laifin cin zarafin kananan yara zai fuskanci hukunci.

Ta kuma gargadi Manoma a fadin jihar da su guji kai Mata gona domin yin aiki, tana mai bayyana haka a matsayin saka mata aikatau. Ta bukaci shugabannin gargajiya da su taimaka wurin kare kananan yara daga cikin zarafi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: