Tinubu bashi da kwarewa a fannin diflomasiyya na duniya – Sule Lamido

0 259

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, kuma daya daga cikin wadanda suka kafa babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Sule Lamido ya bayyana shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu a matsayin wanda bashi da kwarewa a fannin diflomasiyya na duniya.

Lamido ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani ga matsayar da ECOWAS ta dauka kan juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar.

Jawabin nasa na kunshe ne a wani sako da ya wallafa a shafin sa na Facebook mai suna “Nigeria/Niger face off.”

Ya bayyana cewa, a ‘yan makonnin da suka gabata ne, shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya tsinci kansa a tsaka mai wuya dangane da matakin da ya dauka domin warware rikicin juyin mulkin da akayi a jamhuriyyar Nijar.

Ya shawarci shugaban kasar da yayi amfani hikimar tsofaffin shugabannin kasar nan wajen bullo da hanyoyin da suka dace wajen magance wannan matsalar ba tare da zubar da jini ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: