Kwalbati da Gada sun rushe a kauyen Kalajaga da ke kan hanyar Bauchi zuwa Gombe

0 293

Shugaban hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC Dauda Biu, ya shawarci masu ababen hawa da ke bi ta hanyar Abuja zuwa Yola da wadanda ke tafiya daga yankin Arewa maso Gabashin kasar nan zuwa yankin Arewa ta tsakiya da su rika bin wasu hanyoyin daban-daban.

Mista Biu ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da jami’in kula da ilimin jama’a na hukumar CPEO, Bisi Kazeem, ya fitar jiya a Abuja.

Ya ce shawarar ta zama dole biyo bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka samu a sanyin safiyar jiya, wanda ya dauki tsawon sa’o’i ana ta yi.

A cewarsa, an samu rushewar wata Kwalbati da Gada a kauyen Kalajaga da ke kan hanyar Bauchi zuwa Gombe.

A dan haka suna sanar da matafiya cewa, kada suyi amfani da wannan titin.

Shugaban rundunar, ya bukaci jama’a da su ba da hadin kai wajen kauracewa yin amfani da titin, inda ya kara da cewa rundunar za ta ci gaba da fadakar da al’umma akan cigaban da ake samu akan titin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: