Ana sa ran ambaliyar ruwa za ta afku cikin wannan watan a jihar Jigawa

0 665

Sakataren zartarwa na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa (SEMA), Alhaji Haruna Mairiga, ya ce yin hadin gwiwa da kungiyoyi masu zaman kansu zai karfafa ayyukan hukumar.

Ya ce hukumar na bukatar karin kayan aiki kamar manyan motoci na kwashe mutanen da iftila’in ya rutsa da su, da motocin daukar marasa lafiya na agajin gaggawa, da kuma karin tantuna da za su jagoranci ayyukan gaggawa idan iftila’I ya faru.

Sakataren zartarwa, Alhaji Mairiga, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da wakilinmu a karshen mako a Dutse, kan ambaliyar ruwa da ake sa ran za ta afku a wannan watan kamar yadda masana suka yi hasashen.

Mairiga ya ci gaba da cewa, a kwanan baya an horas da su dabarun ceto a Kano kan yadda za su kula da kuma taimaka wa wadanda iftila’in ya shafa, kafin ya faruwa, a lokacin dake faruwa da kuma bayan faruwar iftila’in. Wannan na zuwa ne adaidai lokacin da masana ke cewa Jigawa na cikin jihohin da za a iya samun ambaliyar ruwa a cikin wannan watan na Agusta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: