Tinubu ya sake sauyawa wasu ministoci ma’aikatu, ya kuma bayyana sabon ministan Niger Delta

0 273

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sauyawa Abubakar Momoh ma’aikata daga ma’aikatar matasa ta tarayya zuwa ma’aikatar raya yankin Neja Delta.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun shugaban kasa Ajuri Ngelale.

A cewar Mista Ngelale, nan ba da dadewa ba za a sanar da sabon Ministan ma’aikatar matasa da wasanni ta kasa.

Ya kara cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kuma sake yin garanbawul a ma’aikatun Sufuri, Cikin Gida, Tattalin Arziki da kuma Albarkacin Ruwa kamar haka.

(A) Adegboyega Oyetola an tura shi zuwa ma’aikatar Tattalin Arziki na cikin Ruwa.

(B) An sake tura Bunmi Tunji-Ojo a matsayin Ministan Harkokin Cikin Gida

(C) Sa’idu Alkali ya zama Ministan Sufuri

Bugu da kari, kar kawo yanzu ba a nada sabbin manyan Ministoci a bangaren Man Fetur da iskar Gas ba, amma an nada:

(i) Sen. Heineken Lokpobiri a matsayi Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur

(ii) Ekperipe Ekpo, Karamin Ministan Albarkatun Gas.

Leave a Reply

%d bloggers like this: