Kundin tsarin mulkin Najeriya ya haramta nadin tsoffin gwamnonin da ke karbar fansho mukamin minista

0 286

Kungiyar Kare Hakkokin Tattalin Arziki ta Kasa (SERAP) ta bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya fito fili ya umurci tsaffin gwamnonin da ke rike da mukamin minista a gwamnatinsa da su daina karbar kudaden fansho, da manyan motoci da sauran alawus-alawus daga gwamnatocin jihohinsu bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada su ministoci.

SERAP ta kuma bukace shi da ya umurci tsoffin gwamnonin da su gaggauta mayar da duk wani kudaden fansho da alawus-alawus da suka karba tun bayan barin kujerun su zuwa asusun gwamnati.

Tsofaffin gwamnonin da ke cikin gwamnatin Tinubu a yanzu sune: Badaru Abubakar, Nyesom Wike, Bello Matawalle, Adegboyega Oyetola, da David Umahi.

Sauran sun hada da Simon Lalong, Atiku Bagudu, da Ibrahim Geidam. A wata wasika da mataimakin daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare ya sanya wa hannu, kungiyar ta ce, nadin tsoffin gwamnonin da ke karbar fansho mukamin minista abu ne da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya haramta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: