An bayyana Sanata Akume a matsayin mai fikira, mutunci, samar da hadin kai, aminci da rikon amana a Nigeria

0 246

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya yi kira ga masu rike da mukaman siyasa da masu neman mukaman siyasa da su rika fifita maslaha, hadin kai da cigaban al’umma sama da son kai ko bangaranci.

Shettima ya bayar da shawarar ne a wata liyafar da kungiyar gwamnonin Arewa ta tsakiya ta shirya domin murnar nadin sakataren gwamnatin tarayya Sanata George Akume da kuma nasarorin da aka samu a taron da aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja.

Mataimakin shugaban kasar, wanda ya jinjinawa George Akume a cikin wani sako mai taken ‘rayuwar karramawa.

An bayyana Sanata Akume a matsayin mai fikira, mutunci, samar da hadin kai, aminci da rikon amana a Nigeria, inda ya bukaci shugabannin siyasa su yi koyi da shi. Shettima a wata sanarwa da ya fitar jiya ta hannun Daraktan yada labarai na ofishin mataimakin shugaban kasa Olusola Abiola, ya kuma jaddada muhimmancin sadaukarwa ga masu neman mukaman siyasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: