Buhari ya bayyana alhininsa kan harin da ‘yan bindiga suka kaiwa jirgi mai saukar ungulu a jihar Neja
Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa kan mutuwar wasu sojoji da suka rasa ransu a wani harin kwantan bauna da wasu ‘yan bindiga suka kaiwa jirgin su mai saukar ungulu a jihar Neja.
Buhari, a cikin wata sanarwa da ya fitar jiya ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, ya jajanta wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, da sojojin kasar da kuma iyalan mamacin.
Ya ce, ya yi alhinin hatsarin jirgin saman mai saukar ungulu biyo bayan mummunan harin kwantan bauna da ya faru, inda akayi asarar manyan jami’an tsaron kasar nan. Ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu da adduar samun lafiya ga wadanda suka jikkata.