Gwamna Zulum ya mika tallafin N10M ga sojojin da suka samu raunuka a yakin da ake yi a jihar

0 182

Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya mika tallafin Naira miliyan 10 ga sojojin da suka samu raunuka a yakin da ake yi da masu tayar da kayar baya a jihar.

Kwamishinan yada labarai da tsaro na Borno Usman Tar da babban sakataren gidan gwamnati Mustapha Busuguma ne suka gabatar da kunshin kudaen ga babban hafsan runduna ta 7 dake Maiduguri Manjo-Janar Peter Malla.

A yayin gabatar da jawabin, Mista Tar ya ce kunshin cika alkawari ne da Zulum yayi a lokacin bikin cin abincin rana ga sojoji a Maiduguri, wanda babban hafsan sojin kasa, Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja ya shirya.

Ya bayyana kudurin gwamnatin jihar na ci gaba da baiwa gwamnatin tarayya hadin kai wajen samar da kayan aiki da sauran kayan tallafi domin inganta jin dadin sojojin bisa la’akari da sadaukarwar da suke yi wajen kare martabar yankunan Najeriya. A nasa martanin, babban hafsan runduna ta 7 Manjo-Janar Peter Malla, ya nuna jin dadinsa ga Zulum bisa irin goyon bayan da yake baiwa sojoji a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: