Tsohon dan wasan Jigawa golden star ya rasu yana tsaka da atisaye a filin Kano Pillars

0 1,144

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Jigawa golden star Sabo Captain ya rasu.

Lamarin ya faru ne a safiyar jiya 18 ga watan Yuni, 2023 lokacin da Sabo ya fadi ya mutu a lokacin da yake atisaye a filin wasa na Kano Pillars dake Sabon Gari Kano.

An yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada da misalin karfe 10 na safiyar jiya a birnin Kano.

Rashin nasa ya sa Inter Community Peace LOC sun dage wasannin kwata final da za a yi a jiya na kwanaki 2 saboda jimamin mutuwar tasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: