Mambobin jam’iyyar APC sun bukaci shugaban kasa Bola Tinubu ya kafa kwamitin da zai kare gwamnatin sa daga zagon kasa.

0 242

Mambobin jam’iyyar APC sun bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kafa kwamitin da zai kare gwamnatin sa daga zagon kasa.

Shugaban kungiyar Malam Danjuma Muhammad ne ya yi wannan kiran jiya a Abuja a wani taron manema labarai kan halin da kasa ke ciki.

Ya ce a matsayinsu na ’yan jam’iyya masu goyon bayan shugaban kasa, suna ganin ya dace gwamnati ta kare manufofinta da shirye-shiryenta da ayyukanta don kauce wa tarnaki da suka janyo gazawar gwamnatocin dimokaradiyya da suka gabata a cikin shekaru 24 da suka gabata.

Kungiyar ta shawarci shugaban jam’iyyar APC na kasa, Cif Bisi Akande da Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila; tsohon shugaban hukumar EFCC, Malam Nuhu Ribadu, da kuma mai baiwa shugaban kasa shawara kan ayyuka na musamman, sadarwa da dabaru, Dele Alake, domin su zama mambobi na farko a wannan aiki.

Sauran sun hada da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-rufai; tsohon gwamnan Jigawa, Muhammed Badaru Abubakar; James Faleke, Dr Ene Lilian Ogbole, Festus Keyamo (SAN), Adams Oshiomole, da Bayo Onanuga.

Leave a Reply

%d bloggers like this: