UNICEF da kungiyar editoci ta Najeriya sun sa hannu kan yarjejeniyar kare hakkokin yara a Najeriya

0 71

Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar editoci ta Najeriya sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya domin kare hakkoki da jin dadin yara a Najeriya.

Anyi wannan hadakar ne domin yin amfani da tasirin kafofin watsa labarai wajen haɓakawa da kare haƙƙin yara a duk faɗin ƙasar nan.

Sanarwar da UNICEF ta fitar ta nuna cewa, hadin gwiwar za ta mayar da hankali ne kan bayar da shawarwari da wayar da kan jama’a, da karfafa gwiwar ‘yan jarida, da gudanar da bincike tare, da sanin irin gudunmawar da kafofin watsa labaru ke bayarwa, da kuma yin tasiri kan manufofin tallafawa ‘yancin yara. Yarjejeniyar zata bada himma daga kowane bangare na yin aiki tare ga al’umma da kuma ciyar da rayuwar kananan yara gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: