Sojojin Najeriya da aka tura domin yaki da ta’addanci da masu tayar da kayar baya a arewa maso gabas da arewa ta tsakiya, sun sanar da kama wasu masu garkuwa da mutane uku a yankin Lankaviri dake karamar hukumar Karim Lamido ta jihar Taraba.
Sanarwar wacce rundunar ta wallafa a shafin ta na X a ranar Asabar din da ta gabata, ta ce sojojin a ranar 18 ga watan Afrilu, sun dakile wani yunkurin yin garkuwa da Musa Arewa da wasu masu garkuwa da mutane uku suka yi a kauyen Lankaviri da ke karamar hukumar Karim Lamido. Jihar Taraba.
Rundunar sojin ta ce bayan kama wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne, an kuma kwato bindigogin gida guda uku daga hannunsu. A wani yunkuri na hadin gwiwa tare da mafarauta da sauran jami’an tsaro, sojojin sun gudanar da sintiri domin samarda tsaro ga al’ummomin da ‘yan ta’adda suka shiga.