Uwar gidan shugaban kasa Remi Tinubu ta gana da wata ƴar Chibok da aka ceto

0 364

Uwar gidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu ta gana da ɗaya daga cikin ƴan matan Chibok 276 da ƴan Boko Haram suka sace sama da shekaru tara da suka gabata.

An sace ƴan matan ne a ranar 14 ga watan Afrilu na 2014, lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Uwar gidan shugaba Tinubu ta tarbi Rebecca Kabu tare da uwar gidan matamakin shugaban kasa Nana Shettima.

Misis Remi ta yi wa yarinyar alƙawarin kula da ita da kuma mayar da ita makaranta a duk lokacin da take buƙata.

Ta kuma ce gwamnati ba ta manta da sauran ɗaliban da ke tsare a hannun Boko Haram ba.

Uwar gidan shugaban Najeriyar ta kuma miƙa godiyarta ga ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro da kuma hukumar tattara bayanan sirri ta Najeriya, da sauran dukkan waɗanda suka tallafa wajen kuɓutar da Rebecca.

Sanata Oluremi ta ce idan aka ilmantar da yara masu tasowa, za su taimaka wajen ɗorewar abubuwan ci gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: