Uwargidan shugaban kasa ta yi kiran a kara mayar da hankali wajen inganta rayuwar mata

0 180

Uwargidan shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu ta yi kiran a kara mayar da hankali wajen inganta rayuwar mata.
Ta yi wannan kiran ne a sakonta na taya murnar ranar mata ta bana, inda ta yi nuni da bukatar a bayar da himma wajen tafiya da mata a fannin tattalin arziki da ci gaban al’umma.
Sanata Oluremi Tinubu ta ce; “Lokaci ya yi da za a karfafa gwiwar mata fiye da yadda aka saba a baya. Mata suna da muhimmanci sosai ga kokarin kawo ci gaba, saboda da haka ya kamata a tsara duk wata harkar ci gaba tare da su.
Uwargidan shugaban Najeriyar ta ce tana kallon bunkasa rayuwar mata a matsayin hanyar kawo ci gaban kasa da al’ummar ta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: