Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ce waɗanda suka kashe sojoji a jihar Delta za su fuskanci hukunci, yana mai gargaɗin cewa gwamnatinsa ba za ta amince da kai hare-hare kan sojoji da ababen more rayuwa ba.
Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabannin majalisar dattawan kasar a yayin wani zaman cin abincin buɗe baki a fadar gwamnati a ranar Alhamis.
Tinubu ya ce sojoji za su ci gaba da samun goyon bayan gwamnatinsa wajen kawar da barazanar tsaro a faɗin kasar.
Shugaba yace zasu ci gaba da karfafawa da gwagwarmayar neman ƴancin da haƙƙin zama daya. Tinubu ya shaida wa shugabannin Majalisar Dattawan cewa, mutuncin Majalisar Dokoki dole ne ya ci gaba da wanzuwa, kuma a ko da yaushe gwamnatinsa za ta ƙarfafa hadin gwiwa don ci gaban kasa.