Ministan tsaro ya bada tabbacin cewa nan bada jimawa ba za a kubutar da daliban Kuriga

0 101

Ministan tsaro Muhammed Badaru Abubakar ya bada tabbacin cewa nan bada jimawa ba za a kubutar da daliban Kuriga da aka sace a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Ya yi wannan jawabi ne a ranar Alhamis a Kaduna yayin da yake jawabi ga sojojin da ke yaki da yan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma da sauran sassan kasar nan.

Ministan ya kuma tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za a kama wadanda suka kashe jami’an soji a yankin Okuama na jihar Delta domin fuskantar fushin doka. Ya shaida wa sojojin cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana sane da sadaukarwar da suka yi kuma yana farin ciki da kokarinsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: