Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da cafke wani matashi mai shekaru 25 da haihuwa, Buhari Sule, bisa zargin kashe matar ƙaninsa da kuma raunata ‘yar makwabcinsa a ƙauyen Gunka da ke ƙaramar hukumar Jahun.
Kakakin rundunar SP Shi’isu Adam ya bayyana cewa Buhari ya doke matar ƙaninsa, Ummi Saleh, da guduma, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarta, yayin da Hauwa Alkassim ta samu munanan raunuka.
Rahoton ya ce ana zargin Buhari na fama da matsalolin tabin hankali, kuma jami’an ‘yan sanda za su gudanar da cikakken bincike da kuma gwajin lafiyar kwakwalwarsa domin tantance matsayinsa.
Jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sanda ya bukaci jama’a da su kwantar da hankula tare da bada haɗin kai ga jami’an tsaro domin kammala bincike cikin nasara.